in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Malawi, wata kasa mai zuciya cikin nishadi
2010-07-15 15:54:17 cri

Idan muka ci gaba da ziyara, za mu iya kallon hotuna da bidiyon da ke rataye kan bango wadanda ke nuna kan ni'imtaccen dutsen Mulanje, da sauran wurare na yawon shakatawa. Hotuna na manyan birane guda hudu wato Liongwe, Blantyre, Zomba, Mzuzu suna bayyana kan bunkasuwar kasar Malawi cikin sauri.

Mr. Namon jakadan kasar Malawi da ke kasar Sin ya ce, kasar Malawi tana kudu maso gabashin nahiyar Afirka, kuma tana daya daga cikin kananan kasashen Afirka, amma tana da al'adu masu kyau a Afirka.

Ya ce, "Muna farin ciki saboda halartar bikin EXPO na Shanghai, ya samar wata dama gare mu, kuma yawan jama'ar kasar Sin sun sami damar fahimtar kasar Malawi." Yana fatan mutanen kasar Sin za su ziyarci kasar Malawi, tare da sa kaimi ga musaya da ke tsakanin jama'ar kasashen biyu.

Mr. Salama babban wakilin rumfar kasar Malawi ya bayyana cewa, mutanen kasar Malawi sun yi suna a Afirka saboda suna da kirki da aminai, saboda haka, ana kirar kasar Malawi "zuciyar Afirka cikin nishadi". Babban taken rumfar kasar Malawi shi ne "Ayyuka masu tasiri da basira za su kawo zaman rayuwa mai inganci", wannan shi ne ka'idar da gwamnati da jama'ar kasar Malawi ke tsayawa a kjai a dogon lokaci. Yanzu, kasar Malawi tana kokarin bunkasa aikin gona, manyen gine-gine, da ba da ilmi domin inganta zaman rayuwar jama'a ta kasar Malawi. [Musa Guo]


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China