in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Malawi, wata kasa mai zuciya cikin nishadi
2010-07-15 15:54:17 cri

Ranar 14 ga wata, rana ce ta rumfar kasar Malawi a bikin EXPO na Shanghai, Madam Katsiko ministar kula da yawon shakatawa, da kula da namon daji da al'adu na kasar Malawi da Mr. Jiang Zhengyun mataimakin shugaban wakilan gwamnatin kasar Sin a bikin EXPO sun halarci shagalin ranar rumfar kasar Malawi.

Yayin da Madam Katsiko ke yin jawabi ta nuna godiya ga taimakon da gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasar Malawi. Ta ce, tun da kasashen biyu sun kulla huldar diplomasiyya a shekarar 2007, sun yi hadin gwiwa masu kyau a fannoni daban daban, wannan ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Malawi sosai. Tana tsammani bikin EXPO na Shanghai ya samar da wata dama ga kasar Malawi wajen neman ci gaba kan fannonin jawo jari, da cinikayya, da yawon shakatawa, wannan zai sa kasar Malawi ta iya yin hadin gwiwa da musaya tare da 'yan kasuwa na kasar Sin, haka kuma za ta iya bude kasuwanni a kasar Sin, har ma da kasashen Asiya.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China