in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Malawi, wata kasa mai zuciya cikin nishadi
2010-07-15 15:54:17 cri

Mr. Jiang Zhengyun ya ce, babban taken rumfar kasar Malawi shi ne "Ayyuka masu tasiri da basira za su kawo zaman rayuwa mai inganci", wannan ya yi bayani kan ilmin bunkasuwar birane da cigaban al'adu, sauye-sauyen tsarin tattalin arziki, da musayar da ke tsakanin birane da karkara, da sauyawar yanayi da nauyin da birane suke dauka. A cikin shekaru 2 da kasashen biyu suka kulla huldar diplomasiyya, huldar da ke tsakaninsu tana bunkasuwa yadda ya kamata. Kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Malawi domin shimfida ra'ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa yn hadin gwiwa kan fannonin tattalin arziki da ciniki.

Rumfar kasar Malawi tana yanki na hudu (D) na dakin hadin gwiwa na nahiyar Afirka. Rumfar kasar Malawi ta yi kama da wani kyakkyawan yankin karkara inda za ka ga wata giwa a gefen hagu, kuma akwai wata babbar bishiya a tsakiya, da wani gida irin na Afirka yana kusa da ita kana an ajiye wata katuwar tukunya da wani kifi a ciki da ake kira "Cichlid" yana iyo a ciki.

A cikin rumfar kasar Malawi, ana iya ganin abubuwa na salon hallitu mai dacewa, da rairayi, da zane-zane na Afirka. A yankin nune-nune na zane-zanen sana'o'in hannu, ana iya samu mutum-mutumn da aka yi da itace ko dutse, da abubuwan da aka saka da hannu, da zane-zane. Dukkansu sun nuna tunani na musaman na 'yan kasar Malawi.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China