in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muna fatan kasashen duniya za su kara fahimtar kasar Timor ta gabas ta bikin EXPO na Shanghai, a cewar shugaban kasar
2010-07-14 15:57:02 cri

Kasar Sin kasa ce ta farko da ta kulla huldar diplomasiya da kasar Timor ta gabas. A karkashin kokarin da kasar Timor ta gabas ta yi, gami da samun taimako daga kasashen duniya, ciki har da kasar Sin, yanzu yanayin da kasar Timor ta gabas ke ciki ya zauna da gindinsa. Ramos-Horta ya ce, kasar Timor ta gabas na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, kana tana kokarin samun saurin bunkasuwar tattalin arziki. Ya kara bayyana cewa, 'Yanzu kasarmu na shimfida zaman lafiya da zaman karko. A waje guda kuma, muna samun saurin bunkasuwar tattalin arziki. Yawan karuwar tattalin arzikinmu na matsayin gaba a Asiya, ya yi kamar daidai na kasar Sin. Gaskiya ne mun zabi wata hanya mai dacewa.'

A matsayinta na wata sabuwar kasa, Timor ta gabas, wadda a karo na farko ta halarci bikin EXPO ta ba da kyakkyawar alama a zuciyar masu yawon shakatawa da suka fito daga kasashe daban daban. Rumfar kasar Timor ta gabas ta nuna cewa, yanzu kasar na kokarin samun bunkasuwa ta hanyar tsimin makamashi.

Ramos-Horta ya bayyana cewa, bikin beje koli na duniya na Shanghai ya samar da wata dama ga kasar Timor ta gabas, don ta nuna yanayinsa mai kyau. A kullum jama'ar kasar Timor ta gabas suna kokarin neman kiyaye muhalli, da kare abubuwa masu rai iri daban daban, a yayin da take neman bunkasuwar tattalin arziki, da zaman al'umma, a sa'i daya kuma tana tsayawa tsayin daka kan tabbatar da samun bunkasuwa ta hanyar tsimin makamashi.


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China