A ranar 11 ga wata, Mr. Ramos-Horta ya iso birnin Shanghai, don halartar bikin murnar ranar nune-nune na rumfar kasar. Ya ce, ko da yake na iso birnin Shanghai ba da dadewa ba, amma ko da haka birnin ya sheda kyakkyawar alamar bunkasa kan tattalin arziki. Ya kara bayyana cewa, 'Birnin Shanghai ya ba ni kyakkyawar sura a zuciyata. Birnin Shanghai kuma zai zama wani birnin da ya fi zama na zamani a duniya, da kuma wata cibiyar da ta fi girma a fannin hada-hadar kudi a duniya.'
Bayan haka kuma, shugaban kasar Timor ta gabas, Jose Ramos-Horta ya bayyana cewa, yana fatan ta hanyar bikin baje koli na duniya, mutane daga kasashe daban daban za su kara fahimtar yanayin da kasar Timor ta gabas ke ciki. Ya kara da cewa, 'Muna jin farin ciki sosai don halartar wannan biki a matsayinmu na wata sabuwar kasa. Wannan ne kuma karo na farko da muka halarci bikin EXPO bayan da muka samu 'yancin kai. Na yi imani cewa, masu yawon shakatawa da suka fito daga kasar Sin da sauran kasashe za su kara fahimtar yanayin da kasar Timor ta gabas ke ciki, da al'adu da tarihinmu, da kuma ci gaban da muka samu.'