in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rumfar kungiyar sada zumunci a kasashen Jamus da Sin a bikin baje koli na duniya na Shanghai
2010-06-04 17:07:12 cri

A cikin wannan rumfa, aiki mai ban sha'awa shi ne wasan "gina birni tare" da jami'ar masana'antu ta Aachen ta kasar Jamus ta kera. Idan masu yawon shakawata suka daga hannu sama suka motsa jiki, gine-gine za su fito kan bango a gabansu. Dr. Wolfgang Rohr tsohon karamin jakadan kasar Jamus a Shanghai ya bayyana cewa, "Da farko, za a rarraba mutane 16 su ta yadda za zama wata kungiya, sai za mu dauki hotunannsu. Idan masu yawon shakatawa suka tsaya a bango da ke gabansu, sai za su iya amfani da na'urar kwamfuta wajen gina gine-gine a yadda suke tsaye, tare da dasa itatuwa da samar da ruwa, da wutarlantarki, a karshe kuma, sai wannan gine-gine su zama tamkar wata unguwa."

A yayin da wakilinmu ke yin ziyara a wannan rumfa, ya ga wata tsohuwa tana yin ziyara tare da mijinta. Ta gayawa wakilinmu cewa, "Na gani kuma na gane wadannan fasahohi na zamani, na sami ilmi da yawa daga wadannan kayayyaki da ake kirkiro. Zan gayawa abokaina, wannan rumfa tana da ban sha'awa sosai, al'adun kasar Jamus suna da kyau sosai, mun taba zama a kasar Jamus, zaman rayuwa a kasar Jamus tana da kyau."

Bisa labarin da muka samu, an ce, kasar Sin tana shirya aikin "shekarar kasar Sin" a kasar Jamus na shekarar 2011 zuwa shekarar 2012. Game da haka, Dr. Wolfgang Rohr ya nuna cewa, "muna jiran zuwan wannan aiki da farin ciki" [Musa Guo].


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China