in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rumfar kungiyar sada zumunci a kasashen Jamus da Sin a bikin baje koli na duniya na Shanghai
2010-06-04 17:07:12 cri

Tun daga shekarar 2007, biranen da aikin "Yin ziyara a kasashen Jamus da Sin" ya shafa ya hada da Beijing, da Shanghai, da Nanjing, da Chongqing, da Guangzhou, da Shenyang, da Wuhan. Mutanen kasar Sin da dama sun halarci wannan aiki ta hanyoyi daban daban.

Fadin "rumfar wakilan kungiyar sada zumunci a kasashen Jamus da Sin" da ke yankin C a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai ya kai muraba'in mita 330, kuma ya bude kofa ga masu yawon shakatawa tun daga ran 1 ga watan Mayu zuwa ran 30 ga watan Yuni, ya yi cikakken bayani da kayayyakin nune-nunen fasaha kan babban taken "yunkurin neman bunkasuwa da ya dace da birane". An gina wannan rumfa da gorori 96 kuma tsayinsu ya kai mita 8, kuma wadannan gorori wuta ba ta cinsu, an hada su da wani karfen da kasar Jamus ta kera, sannan wannan gini yana da karfi sosai, kuma za a iya raba ginin nan domin sake yin amfani da gora da karfe, wannan zai kiyaye muhalli sosai.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China