in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rumfar kungiyar sada zumunci a kasashen Jamus da Sin a bikin baje koli na duniya na Shanghai
2010-06-04 17:07:12 cri

Idan ka gama ziyara a rumfar kasar Jamus a bikin EXPO na Shanghai, sannan ka ci gaba da tafiya da kafa na wasu 'yan mintoci, za ka ga wani gini na benaye biyu da aka gina da gora. Wannan gini shi ne "rumfar kungiyar sada zumunci a kasashen Jamus da Sin" da aka gina a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai.

"Yin ziyara a rumfar kasashen Jamus da Sin" wani aikin sada zumunci tsakanin kasashen biyu da aka shafe shekaru 3 ana yinsa. Tsohon shugaba Hosrt Kohler ya nuna yabo sosai ga aikin "sada zumunci a tsakanin kasashen Jamus da Sin", ya ce, "Yunkurin neman bunkasuwa da ya dace a birane shi ne babban take na aikin 'yin ziyara tare a kasashen Jamus da Sin', wannan aiki ya shafe shekaru uku ana yinsa, shugaba Hu Jintao na kasar Sin da ni kaina muna kula da wannan aiki. Za a yi wannan aiki a bikin EXPO na Shanghai, kuma shi ne aiki mafi girma kuma mafi tsawon lokaci da kasar Jamus ta yi a ketare. Abin farin ciki shi ne, wannan aiki ya sada zumunci sosai tsakanin jama'ar kasashen Jamus da Sin."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China