in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaran kasar Sin da na Afirka sun zama abokai a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai
2010-06-03 14:04:34 cri

Wakokin sun sa yaran Afirka sun san wasu yaran kasar Sin, da kuma garinsu, wato filin ciyayi na Hulunbei'er. Haka kuma, da farko yaran kasar Sin sun kalli fuskokin yaran dake murmushi. Yaro Balaking na kabilar Mongoliya wanda ya kai shekaru 11 da haihuwa ya gaya wa wakiliyarmu cewa, wannan ne karo na farko da ya sadu da yaran Afirka. Ya ce yana sha'awar gashin kan yaran Afirka.

Sakamakon bikin Expo na Shanghai, yaran kasar Sin da na kasar Malawi sun sadu da juna. Shekarunsu na haihuwa suna daidai da juna, kuma suna da sha'awa iri daya. A lokacin da ake murnar ranar yara ta duniya, sun taya juna murna. "Taya ku murnar ranar yara. Muna fatan za ku iya ziyartar garinmu. A garinmu, za ku iya shan ti da madara, kuma za mu yi wasa a filin ciyayi."

Yaran Afirka kuma sun rera wakoki domin taya yaran kasar Sin murnar ranar yara. (Sanusi Chen)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China