in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaran kasar Sin da na Afirka sun zama abokai a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai
2010-06-03 14:04:34 cri

A kwanan baya, da suka ji an ce, wasu yaran kasar Sin ma suna nuna wasannin wakoki da kide-kide a farfajiyar bikin Expo na Shanghai, yaran makatantar Yuantong ta kasar Malawi sun nuna farin ciki sosai. Sabo da haka, da suka kammala nune-nunensu, nan da nan suka tafi filin nune-nune da kungiyar Hulunbei'er mai launuka 'yan armashi ta yaran kasar Sin take, inda suka zauna a gaban dandalin. Lokacin da yaran kasar Sin suke waka da taka rawa har na tsawon sa'o'i biyu, wadannan yaran Afirka 20 ko fiye sun zuba ido kan takwarorinsu wadanda suke dandalin, kuma sun ji dadin wakokin da yaran kasar Sin suka rera. Yaro Blessings Scale na kasar Malawi ya ce, "Su kanana ne, amma sun iya rera wakoki sosai. Ban taba sauraron wakoki masu dadin ji kamar wadannan ba. Ko da yake ban gane abin da suke rerawa ba, amma wakokinsu sun burge ni. Ina son zama abokansu, kuma ina son gayyatarsu zuwa garinmu."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China