in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaran kasar Sin da na Afirka sun zama abokai a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai
2010-06-03 14:04:34 cri

Kafin ranar yara ta duniya, kungiyoyin nune-nunen wasannin kwaikwayo na yara guda biyu sun gana a farfajiyar bikin Expo na Shanghai. Daya daga cikinsu ita ce kungiyar Hulunbei'er mai launuka, wato kungiyar 'yan amshi ta yaran kananan kabilun kasar Sin ta farko, dayar daban ita ce kungiyar 'yan makarantar Yuantong ta kasar Malawi. "Ni ne Balaking, kuma na zo ne daga filin ciyayi na Hulunbei'er, wani dan kabilar Mongliya ne. A kan ga gajimare fari tare da sararin sama mai launin shudi, kuma akwai tsuntsaye da furanni iri iri a garinmu. Sannan muna kiwon shannu da awaki da tumaki da kuma rakuma." Ni ne Blessings Scale da na zo daga kasar Malawi a nahiyar Afirka. A garinmu, mu kan noma masara da kayayyakin lambu. Kuma a garinmu akwai babban kwari na gabashin Afirka. Ban taba zuwa filin ciyayi ba, ina son na kai ziyara gidan Balaking."

Jama'a masu sauraro, shekarun wadannan yara na haihuwa suna tsakanin 5 zuwa 15, kuma suna zaune a wurare daban daban, sannan suna magana da harsuna daban daban. A da, ba su san juna ba, balle saduwa da juna a wani wuri.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China