in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru sun tattauna batun sauyin yanayin duniya a nan Beijing
2010-05-25 19:55:37 cri

Ibrahim: Mr. Cherif Rahmani, ministan kula da filaye kasa da muhalli da harkokin yawon bude ido na kasar Aljeriya ya amince da ra'ayin Mr. Xie Zhenhua, inda ya jaddada cewa, yin musayar fasaha tana da muhimmanci sosai ga kasashen Afirka wajen raya tattalin arziki maras gurbata muhalli da fama da sauyin yanayin duniya.

"Ya kamata a kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa da kara yin musayar fasahohin zamani. Yin musayar fasahohin zamani yana da muhimmanci sosai ga kasashen Afirka. Dole ne a yi watsi da fasahohin da ba su dace ba."

Sanusi: A lokacin da ake kokarin rage fitar da abubuwa masu dumama yanayi, raya tattalin arziki maras gurbata muhalli ya zama zabi na wajibi ga dan Adam domin tabbatar da ingancin yanayin duniyarmu. Mr. Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya ya yaba wa amfanin tattalin arziki maras gurbata muhalli cewa, "Ko za mu iya ceton muhallin duniyarmu? Ko za mu iya bunkasa tattalin arzikinmu ba tare da kasala ba? Tabbas ne za mu iya yin haka. Wannan ne dalilin da ya sa muke kokarin bunkasa tattalin arziki maras gurbata muhalli. Dole ne mu dauki matakan fama da sauyin yanayin duniya."  (Sanusi Chen)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China