in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru sun tattauna batun sauyin yanayin duniya a nan Beijing
2010-05-25 19:55:37 cri

Ibrahim: A gun wannan taro, Mr. Michael Church, ministan kula da muhalli na kasar Grenada ya ce, sauyin yanayin duniya yana yin illa sosai ga kasashen tsibirai, kamar Grenada, inda ya ce, "Kasarmu Grenada tana fama da illar da ba a taba ganin irinta ba a da sakamakon sauyin yanayin duniya. A da, a kan samu aukuwar bala'i daga indallahi mai tsanani sau daya a cikin kowane shekaru hamsin, amma a cikin 'yan shekarun da suka gabata, ana samun irin wadannan bala'u daga indallahi kusan a kowane lokaci, kuma sun yi ta kara tsanani. Kasar Grenada da sauran kananan kasashen tsibirai, kamar kasashen Kiribati da Tuvalu da Maldives dukkansu suna fuskantar matsalar sauyin yanayin duniya. Yanzu, babu sauran wata hanyar da ta rage illa, dukkan kasashen duniya su dauki matakan magance irin wannan sauyi cikin hadin gwiwa."

Sanusi: Lokacin da sauyin yanayin duniya ya yi tsanani, batun yadda za a iya yin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli ya zama wani babban batu a gaban kasashen duniya. Amma yaya za a iya raba irin wannan nauyi a tsakanin kasashe masu wadata da kasashe masu tasowa? Har yanzu ra'ayoyi sun sha bamban. A gun taron da aka yi a nan birnin Beijing, Mr. Xie Zhenhua, mataimakin shugaban kwamitin yin gyare-gyare da ci gaban kasar Sin ya sake jaddada cewa, "Lokacin da kasashe masu wadata suke bunkasa masana'antu a cikin shekaru 200 ko fiye da suka gabata, sun fitar da dimbin abubuwa masu dumama yanayin duniya. Wannan ne muhimmin dalilin da ya sa aka samu sauyin yanayin duniya a yanzu. Sabo da haka, ko shakka babu, dole ne su sauke nauyi da zai zama tarihi wajen kara rage fitar da abubuwa masu dumama yanayin duniya. Yanzu, a galibi dai, kasashe masu tasowa suna matakin farko wajen bunkasa masana'antu. Idan an kayyade damarsu ta neman ci gaba, wannan bai dace ba, kuma babu ba a musu adalci ba. Ba ma kawai kasashe masu wadata suna da arziki ba, har ma suna da fasahohin kere-keren da babu sinadarin Carbon sosai. Amma kasashe masu tasowa ba su da irin wannan arziki, balle fasahohin zamani da ake bukata, amma suna da nauyin raya tattalin arziki da fama da talauci. Wannan ne me ya sa dole ne kasashe masu wadata suka kasance a kan gaba wajen rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, a waje daya, dole ne su samar da tallafin kudi da fasahohin zamani ga kasashe masu tasowa domin raya tattalin arziki ba tare da wani cikas ba, kuma ba tare da gurbata muhalli ba."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China