
Ibrahim: Tun daga ran 7 zuwa ran 9 ga watan Mayu, cibiyar musayar tattalin arzikin kasashen duniyar ta kasar Sin, da ta yi suna sosai a kasar wajen samar da shawarwari wajen neman ci gaban kasar, ta shirya taron yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa kan batun raya tattalin arziki da zai kasa gurbata muhalli da kokarin fama da sauyin yanayin duniya. Jami'an gwamnatocin kasashe daban daban da wakilan kungiyoyin kasa da kasa sun halarci taro, kuma sun tattauna da kuma musayar ra'ayoyi kan batun sauyin yanayin duniya.
Sanusi: Mahalarta taron suna ganin cewa, ya kamata kasashe mawadata da kasashe masu tasowa dukkansu su bayar da gudummawa kamar yadda ya kamata kan wannan batu, kuma ya kamata su yi kokarin rage fitar da abubuwa masu dumama yanayin duniya da raya tattalin arziki maras gurbata muhalli bisa ka'idojin "sauke nauyi tare bisa ga nauyin da aka dorawa kowane bangare".
1 2 3