in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Baoding yana neman ci gaba bisa tattalin arziki da ba sinadarin Carbon sosai
2010-05-10 09:46:18 cri

Sanusi: Lokacin da ake kokarin canja tunanin jama'a, ana kuma kokarin daukar matakan rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli a birnin Baoding. Ya zuwa karshen shekarar 2009, an riga an yi kokarin yin amfani da na'urori masu aiki da makamashen hasken rana a tituna da gine-gine da unguwannin da jama'a ke zauna da lambunan shan iska da dai sauransu. Yanzu ana amfani da batura masu aiki da hasken rana a cikin fitilun dake ba ababan hawa hannu da fitilun da aka sanya a tituna. A cikin unguwannin jama'a ma ana amfani da fitilu masu aiki da makamashin hasken rana. Sakamakon wannan mataki, yawan wutar lantarki da aka yi tsiminsu a birnin Baoding a kowace shekara ya kai kilowatts miliyan 19.

Ibrahim: Bugu da kari, ana kokarin raya masana'antun samar da batura masu aiki da makamashin hasken rana a birnin Baoding a 'yan shekarun da suka gabata. Ya zuwa yanzu yawan irin wadannan masana'antu ya kai fiye da 1200 a birnin.

Sanusi: Kamfanin Yingli mai hannu jari dake samar da kayayyaki marasa gurbata muhalli kamfani ne da ke yin batura masu aiki da hasken rana. Mr. Wang Shiyuan daya daga cikin shugabannin kamfanin ya gaya wa wakilinmu cewa, dukkan fitilun tituna da fitilun dake ba ababan hawa hannu da aka sanya a titunan birnin Baoding, fitilu ne masu aiki da hasken rana da kamfanin Yingli ya samar, inda Mr. Wang ya ce, "Muna kokarin samar da kayayyakin da za a iya yin amfani da su a gine-gine da tsarin harkokin zirga-zirga na birni da ayyukan da suke da nasaba da zaman rayuwar jama'a da wuraren da ke nune-nunen al'adu. Alal misali, muna nazarin batura masu aiki da hasken rana da za a iya sanya su a jikin motoci. Mun riga mun kulla kwangilolin samar da irin wadannan batura ga kamfanoni dake kera motoci."

Ibrahim: Abin da wannan kamfani yake jin alfahari shi ne ya zama kamfani na farko a kasar Sin, kuma kamfanin samar da sabbin kayayyaki na farko da ya samu izinin tallafawa gasar cin kofin kwallon kafa na FIFA da za a yi a kasar Afirka ta kudu a shekara ta 2010. Bisa kwangilar da aka kulla, kamfanin Yingli zai samar da batura masu aiki da hasken rana ga sansanonin gwaje-gwaje 20 na gasar cin kwallon kafa ta FIFA da za a yi a kasar Afirka ta kudu. (Sanusi Chen)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China