in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Baoding yana neman ci gaba bisa tattalin arziki da ba sinadarin Carbon sosai
2010-05-10 09:46:18 cri

Ibrahim: A shekarar 2008, asusun halittu na duniya ya zabi birnin Baoding na lardin Hebei da ke arewacin kasar Sin ya zama daya daga cikin biranen da ake gwada bunkasa shirye-shiryen da ke fitar da abubuwa masu dumama duniya, wato sanadarin Carbon ba su da yawa. Yanzu, lokacin da ka ziyarci wannan birni, za ka gano cewa, ra'ayin rage fitar da abubuwa masu dumama duniya yana tasiri ga zaman rayuwar jama'a da ci gaban birnin har ma da tattalin arzikinsa. Yanzu, bari mu shiga wannan birni domin mu ga yadda ake tafiyar da wannan shiri na rage fitar da abubuwa masu dumama duniya a birnin Baoding.

Sanusi: Jama'a masu sauraro, wakar da kuka saurara wata waka ce game da yadda ake kokarin rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da daliban makarantar firamare da ke shiyyar raya fasahohin zamani ta birnin Baoding suka rera. Malaman wannan makaranta su ne suka tsara wannan waka da kansu, inda aka bayyana yadda za a yi tsimin wutar lantarki da ruwa da kiyaye ingancin muhalli da makamatansu.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China