in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Baoding yana neman ci gaba bisa tattalin arziki da ba sinadarin Carbon sosai
2010-05-10 09:46:18 cri

Irin wannan matakin da aka dauka ya samu karbuwa a gun yara. An Bohen, wani dalibi ne da ke aji biyu a makarantar ya gaya wa wakilinmu cewa, "Alal misali, muna amfani da wasu kayayyakin da aka jefar a bola domin kera wasu kananan kayan wasa da hannu. Sannan mun halarci aikin 'sa'a daya a duniyarmu' da aka yi. Ni ma na halarci wannan aiki. Ni da iyayena mun kashe talibijin da kuma katse wutar lantarki, sai muka kunna kyandir. Mun yi farin ciki sosai."

Ibrahim: Madam Gao Huijuan, shugabar wannan makaranta tana ganin cewa, koyar da ilmin rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli ga yara, ba ma kawai yara za su iya samun kyakkyawar al'adar zaman rayuwa ba, har ma abin da ya fi muhimmanci shi ne aikin da yara suka yi zai iya yin tasiri ga wani iyali, inda madam Gao Huijuan ta fadi cewa, "Muna kokarin yada irin wannan ilmi ga iyalan dalibanmu. Mun nemi yara da su koma gida da ilmin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, kuma za su bukaci iyayensu da su yi kokarin tsimin makamashi da tabbatar da ingancin muhalli. Yanzu wasu iyalai sun gaya mana cewa, 'ya'yansu su kan bukace su da su yi tsimin ruwa da wutar lantarki da dai sauransu."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China