in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Hai Bao" zata jagorance ku wajen yin ziyara a babban dakin nune-nune na hadin-gwiwar kasashen Afirka a yayin bikin EXPO
2010-04-23 17:15:07 cri

Dakin nune-nune na tarayyar Najeriya ya kunshi rumfuna biyar, wadanda suka shafi harkokin tattalin arziki, da al'adu, da tarihi, da wasannin motsa jiki, da abinci da sauransu, inda za'a yi amfani da fayafayan bidiyo da sauran kayayyakin zamani wajen nuna halin da ake ciki a Najeriya, gami da bunkasuwarta. A yayin bikin EXPO kuma, Najeriya zata shirya bukukuwa iri-iri a ranar kaddamar da dakinta, da ranar samun 'yancin kanta, gami da dandalin tattaunawa kan harkokin cinikayya da zuba jari da za'a yi a watan Agusta. Haka kuma hukumomin jihohi 36 na tarayyar Najeriya zasu shirya ayyuka da dama masu salon musamman na kabilu da al'adu, a kokarin nuna wata kyakkyawar kasar Najeriya.

To, masu sauraro, yanzu ga tambayoyi biyu da zama saka muku a yau. Tambaya ta farko, a cikin babban dakin nune-nune na hadin-gwiwar kasashen Afirka, baya ga rumfar kungiyar tarayyar Afirka, akwai rumfuna nawa ne na sauran kasashe? Tambaya ta biyu a yau ita ce, wace irin alama ce ta dakin nune-nune na tarayyar Najeriya? Muna jiran amsoshinku da wannan adireshi:

China Radio International

Jakar gidan waya, wato PMB 758

Garki, Abuja, Najeriya

Allah ya ba mai rabo sa'a!(Murtala)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China