in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Hai Bao" zata jagorance ku wajen yin ziyara a babban dakin nune-nune na hadin-gwiwar kasashen Afirka a yayin bikin EXPO
2010-04-23 17:15:07 cri

Idan ka shiga cikin wannan daki, za ka ga manyan duwatsu, da babbar hamada, da yankin ciyayi mai fadin gaske, da kungurmin daji, da nau'o'in tsire-tsire, gami da dabbobi iri daban-daban na nahiyar Afirka. Dadin dadawa kuma, Afirka na daya daga cikin tushen asalin al'adun dan Adam, shi ya sa bisa babban take na bikin EXPO na Shanghai, wato "birni mai kayatarwa, da rayuwa mai inganci", za'a nuna yadda biranen Afirka suke a wannan dakin nune-nune.

Baya ga abubuwan gargajiya, a wannan babban dakin nune-nune na hadin-gwiwar kasashen Afirka kuma, masu kallo zasu iya ganin bunkasuwar biranen zamani na kasashen Afirka. Alal misali, a rumfar Jamhuriyar Nijer, za'a iya ganin yadda tsarin biranen kasar yake, da albarkatun da Allah ya hore musu, gami da zaman rayuwar mazauna biranen, ta yadda za ka iya kara fahimtar yadda biranen Nijer ke samun bunkasuwa.

Bayan haka kuma, bari in jagorance ku zuwa dakin nune-nune na tarayyar Najeriya. Babban take na wannan daki shi ne "biranenmu: kasancewar abubuwa iri-iri cikin zaman jituwa", kuma "Dutsen Zuma" zai zama alama ga dakin Najeriya.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China