in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Hai Bao" zata jagorance ku wajen yin ziyara a babban dakin nune-nune na hadin-gwiwar kasashen Afirka a yayin bikin EXPO
2010-04-23 17:15:07 cri

Assalam alaikum! Masu sauraro, sunana "Hai Bao", wato 'yar tsana dake kawo alheri ga bikin baje-koli na kasa da kasa a birnin Shanghai. A cikin shirinmu na yau, bari in jagorance ku zuwa babban dakin nune-nune na hadin-gwiwar kasashen Afirka dake farfajiyar bikin EXPO na Shanghai, daga baya kuma mu bayyana muku yadda dakin nune-nune da tarayyar Najeriya ta kama yake. Kamar yadda muka saba yi, a karshen wannan shiri, bari mu gabatar muku da tambayoyi guda biyu. Tambaya ta farko, a cikin babban dakin nune-nune na hadin-gwiwar kasashen Afirka a yayin bikin EXPO, baya ga rumfar kungiyar tarayyar Afirka, akwai rumfuna nawa ne na sauran kasashe? Tambaya ta biyu a yau ita ce, wace irin alama ce ta dakin nune-nune na tarayyar Najeriya? To, yanzu ga cikakken bayaninmu.

Babban dakin nune-nune na hadin-gwiwar kasashen Afirka, daki ne na hadin-gwiwa wanda ya fi girma, kuma ke kunshe da kasashe mafi yawa a cikin tarihin bikin baje-koli na EXPO, ya hada rumfunan kasashen Afirka 42, gami da na kungiyar tarayyar Afirka. Fadin dakin nune-nune na hadin-gwiwar kasashen Afirka ya zarce murabba'in mita 26000, wanda girmansa ya kai filayen wasan kwallon kafa guda 3 da rabi.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China