Kuma mista Pang Chenmin ya gabatar da cewa, bayan abkuwar bala'in girgizar kasa, an tinkari matsaloli da yawa kamar su hanyoyi marasa kyau, da wurin da ya yi tsayi da yawa da dai sauransu don ba da tabbacin samar da kayayyakin ceto. Jami'an aikin ceto za su ba da kayayyakin agaji a matakan larduna da gundumomi da kauyuka bi da bi. Masu sa ido da hukumomin bincike za su sa ido kan wannan aiki. A halin yanzu dai, ana samar da kayayyakin yadda ya kamata.
Bugu da kari, Mista Pang ya yi nuni da cewa, za a gaggauta gina gidaje ga mutanen dake fama da bala'in don tsugunar da mutane mafi yawa. Yawan mutane na kabilar Tibet a yankin ya kai kashi 93 cikin dari. Game da haka, Pang ya ce, za a farfado da yankin bisa al'adun kabilu. "Da farko, za a tsugunar da jama'a bisa al'adun kabilu. Na biyu, za a shirya wurin zama bisa ilimin kimiyya. Na uku shi ne ana fatan za a gaggauta zaman rayuwar jama'a yadda ya kamata. A karshe, dole ne a kiyaye kwanciyar hankali a yankin."