Ya zuwa ran 21 ga wata da karfe 5 na yamma, mutane 2183 sun rasa rayukansu sakamakon bala'in girgizar kasa mai karfin digiri 7.1 da ya abku a ran 14 ga wata a gundumar Yushu ta lardin Qinghai na kasar Sin, kuma mutane sama da dubu 100 suna fama da bala'in. Pang Chenmin, kakakin ma'aikatar kula da harkokin jama'a kuma mataimakin shugaban hukumar aikin ceto ya gabatar da cewa, ya zuwa yanzu dai, an yi jigilar tantuna kimanin dubu 50 da rigunan sanyi fiye da dubu 160, da barguna kimanin dubu 200 zuwa yankin. Kasancewar ana fama da ruwan sama da kankara a yankin dake fama da bala'in, shi ya sa, ma'aikatar kula da harkokin jama'a da sauran hukumomin suka samar da kayan hura wuta kimanin dubu 7 zuwa yankin. "A cikin watanni uku masu zuwa tun daga abkuwar bala'in girgizar kasa zuwa, za mu dauki matakin samar da kudi yuan goma da hatsi kilogiram 0.5 ga mutanen dake fama da bala'in a kowace rana."