in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Hai Bao" za ta gaya muku labaru game da bikin baje koli na EXPO
2010-04-22 14:08:11 cri

Haka kuma, giyar Moutai da kasar Sin ta samar ta samu lambar yabo ta zinariya a yayin bikin baje koli na kasa da kasa da aka yi a Panama a shekarar 1915. Akwai wani labarin da ya nuna yadda giyar Moutai ta samu lambar yabo ta zinariya. A wancan lokaci, an sanya giyar Moutai a cikin wasu tukwane, kuma an adana su tare da atamfa da wake da man girki wadanda ba su yi farin jini a wajen mutane ba. Amma lokacin da aka yi kacici kacici a tsakanin giya har ya kare, ba wanda ya mai da hankali kan giyar Moutai. Ma'aikatan kasar Sin sun nuna damuwa sosai. Wata rana, wasu alkalai sun shiga dakin nuna kayayyakin kasar Sin, sai wani ma'aikacin kasar Sin mai wayo ya dauki wata tukunya ya jefa ta kasa har ta fadi ta fashe, nan da nan kyamshin giyar Moutai ya jawo hankalin dimbin masu yawon bude ido, wadannan alkalai ma sun ji mamaki. Sakamakon haka, daga karshe giyar Moutai ta samu lambar yabo ta zinariya.

Bikin baje-koli na kasa da kasa da za a yi a birnin Shanghai, shi ne karo na 41 da aka shirya irin wannan biki, kuma shi ne karo na farko da kasar Sin ta shirya bikin baje koli na duniya na EXPO, kana karo na farko da aka shirya shi a wata kasa mai tasowa. Babban taken wannan bikin baje koli na kasa da kasa na Shanghai shi ne "birni mai kayatarwa da rayuwa mai inganci". Yanzu, yawan mutanen da suke zaune a birane yana ta karuwa cikin sauri, wato yawansu ya riga ya kai rabin jimillar mutanen da suke zaune a duniyarmu. Sabo da haka, yadda za a raya birane a nan gaba wata matsala ce da dole ne kowa ya yi nazari a kai. Tabbas ne kayayyakin da suke rage fitar da abubuwa masu dumama duniyarmu da tunanin rage abubuwa masu gurbata muhalli da kuma kayayyakin zamani za su jawo hankalinmu sosai.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China