A shekarar 1851, shi ne karo na farko da aka shirya bikin baje koli na kasa da kasa na EXPO a lambun shan iska na Hyde dake birnin London na kasar Britaniya, inda aka nuna kayayyaki iri iri, ciki har da inji mai aiki da tururin ruwa da injin jirgin kasa da inji mai daga kaya da yawansu ya kai fiye da dubu dari 1 da kasar Britaniya ta samar da su bayan ta ci nasarar raya masana'antu.
Jama'a masu sauraro, yanzu lemon Coca-Cola lemo ne da jama'a suke son sha, amma ko ka san cewa, Coca-Cola ya soma yin suna ne sakamakon halartar bikin baje koli na duniya na EXPO da aka yi a birnin New York da kamfanin ya yi a shekarar 1964? Kuma a yayin wannan biki ne aka kafa lambun shan iska na Disney da kowane yara a duniya ke son zuwa.