in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi zaman makoki domin nuna alhini ga mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa
2010-04-21 18:43:23 cri

A ran nan da karfe 10 na safe kuma, motoci da jiragen kasa na wurare daban daban na lardin Qinghai sun yi ta kada kararawa, kuma an yi ta harbar bingida a matsayin ta'aziyya. Shugabannin kasar Sin tun daga Hu Jintao da Jiang Zeming, Wu Bangguo da Wen Jiabao da jama'ar kasar sun yi tsit a birnin Beijing don nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu. Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bayyana cewa, "Domin nuna alhini ga 'yan uwanmu da suka mutu sakamakon bala'in girgizar kasa da ya auku a gundumar Yushu, don Allah yanzu a tashi kuma yi tsit."

A ran nan kuma, a garin Jiegu na gundaumar Yushu, inda aka fi fama da tsananin bala'in, jama'a 'yan kabilun Tibet da Han fiye da 1000 sun je wurin shirya bikin ta'aziyya don yin juyayin mutuwar mutanen. Buchung Drolma, wata tsohuwa mai shekaru 60 da doriya a duniya ta tsaya a gaban mutane masu nuna ta'aziyya. Ta gaya wa wakilinmu cikin bakin ciki, cewar "mutane masu dimbin yawa sun mutu, dukkan makwabtanta sun rasa rayukansu, ina bakin ciki kwarai da gaske. Na zo wurin ne domin nuna alhinin rashin su."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China