in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi zaman makoki domin nuna alhini ga mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa
2010-04-21 18:43:23 cri

Bala'in girgizar kasa da ya auku a ran 14 ga wata a gundumar Yushu ta lardin Qinghai na kasar Sin ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 2000, yayin da wasu fiye da dubu 12 suka jikkata. A ran 21 ga wata wato bayan kwanaki 7 da abkuwar bala'in, an yi zaman makoki a duk fadin kasar Sin domin nuna ta'aziyya ga mutuwar Sinawa 'yan kabilu daban daban. Wurare daban daban na Sin da kuma ofisoshin jakadancin kasar da ke ketare sun sauko da tutocin kasar zuwa rabin sanda. Haka kuma an dakatar da dukkan shagulgula. Wannan shi ne karo na biyu da aka yi zaman makoki a duk fadin kasar Sin don jama'a da suka mutu sakamakon abkuwar wani bala'i daga indallahi bayan wata mumunar girgizar kasa ta gundumar Wenchuan a shekara ta 2008.

A ran 21 ga wata da sassafe, a filin Tian'anmen na birnin Beijing, an daga tutar kasar Sin tare da yin taken kasar, bayan da tutar ta isa karshen sanda, an sauko da ita sannu a hankali. An saukar da tutar kasa zuwa rabin sanda ne domin nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu a cikin bala'in girgizar kasa na gundumar Yushu.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China