in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin ceto jama'a daga bala'in girgizar kasa ya nuna yadda kasar Sin ta samu nasara wajen tsara shirin ko ta kwana
2010-04-20 17:35:21 cri

Haka zalika kuma, ayyukan da gwamanatin kasar Sin ta yi wajen tinkarar bala'in girgizar kasa sun sa aka gano wata kasar da ta kware waje tinkarar matsalolin da suka bullo ba zato ba tsammani. Bala'in ya sa shugabannin kasar Sin da dukkan al'ummmar kasar sun kara zama tsintsiya madaurinki daya, ta yadda suka samu nasara kan fannoni daban daban, da kuma daidaita ayyuka bisa wani tsari mai nagarta. Sa'an nan, bayan da ya ji labarin aukuwar girgizar kasa, Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya koma gida daga ziyarar da yake yi a waje cikin hanzari, kamar yadda ya ce, 'a lokacin da muke fama da matsaloli, ina so in zama tare da jama'ar kasarmu'. A nasa bangaren kuma, Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin, ya dage ziyarar da zai kai kasashen waje, nan da nan, ya tafi wuraren da girgizar kasa ta ritsa da su, kamar yadda yake cewa 'zan yi gasar gudu da lokaci, domin na ba jama'ar wurin kwarin gwiwa da karfin zuciya'. A sa'i daya kuma, gwamnatocin wurare daban daban na kasar Sin, kamarsu Chongqin, da Yunnan, da Xinjiang, da dai sauransu, sun tura kungiyoyi masu kula da aikin ceto zuwa gundumar Yushu inda aka samu aukuwar girgizar kasa. An tura manyan motoci da dama zuwa gundumar, wadanda ake yin amfani da su wajen aiwatar da aikin ceto, da samar da jinya, da kuma kayayyakin agaji. (Bello Wang)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China