in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin ceto jama'a daga bala'in girgizar kasa ya nuna yadda kasar Sin ta samu nasara wajen tsara shirin ko ta kwana
2010-04-20 17:35:21 cri

Shekaru 2 da suka wuce, yayin da ta yi kokarin tinkarar girgizar kasa da ta auku a gundumar Wen'chuan ta lardin Si'chuan na kasar Sin, gwamnatin kasar Sin ta samu babban yabo saboda aiwatar da aikin ceto cikin gaugawa. Sai dai a wannan karo, kasashen duniya sun gano wata kasar Sin da ke gudanar da aikin ceto cikin hanzari. Game da ayyukan da aka gudanar bayan da aka samu labarin aukuwar girgizar kasa: wato mintoci 20 kawai bayan aukuwar bala'in, hukumar binciken girgizar kasa ta kasar Sin ta mika rahoto ga majalisar gudanarwar kasar, nan da nan majalisar ta kafa ofishin ba da jagorancin aikin ceto, haka kuma ta tura jami'ai zuwa wurin da bala'in ya shafa. A sa'i daya kuma, sassa daban daban na gwamnatin kasar kamarsu ma'aikatar kula da zaman rayuwar jama'a, da ma'aikatar lafiya, da ma'aikatar kula da aikin sufuri da jigilar kaya, da dai sauransu, sun fara gudanar da shirin ko ta kwana, ta yadda suka dauki matakai cikin hanzari. Yadda aka aiwatar da ayyukan cikin hanzari ya sa an samu isashen lokaci domin a aiwatar da aikin ceto mai inganci. Ga misalin an mayar da aikin sufuri da sadarwa ba dare ba rana bayan aukuwar bala'in, haka ma bangaren aikin samar da wutar lantarki. Daga baya kuma, cikin sa'o'i 72 bayan abkuwar bala'in, an kai mutanen da suka samu raunuka masu tsanani zuwa asibitocin sauran wurare inda za a yi musu jinya.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China