in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin ceto jama'a daga bala'in girgizar kasa ya nuna yadda kasar Sin ta samu nasara wajen tsara shirin ko ta kwana
2010-04-20 17:35:21 cri

A ranar 14 ga wata, an samu aukuwar babbar girgizar kasa da karfinta ya kai maki 7.1 a bisa ma'aunin Richter a gundumar Yushu ta lardin Qinghai da ke yammacin kasar Sin. Sa'o'i 72 biyo bayan abkuwar bala'in, gwamnatin kasar Sin ta tura masu kula da aikin ceto fiye da dubu 15 zuwa wurin da girgizar kasa ta shafa, inda suka zakulo mutane fiye da dubu 17 daga baraguzan gidaje. Sa'an nan an tsugunar da jama'ar da bala'in ya shafa rumfunan da aka tsanadar, inda ake samar musu abinci da tsabtaccen ruwa. Wadanda suka kamu da cututtuka kuma, ana musu jinya ba tare da bata lokaci ba. Ganin yadda gwamnatin kasar take kula da aikin kubutar da jama'a da kyau, abin da ya sa ake nuna amincewa kan ci gaban shirin ko ta kwana da kasar ta tsara domin tinkarar matsalolin da ka iya biyo baya.
1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China