in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Hai Bao" za ta jagorance ku wajen yin ziyara a rumfar kasar Sin ta bikin baje koli na kasa da kasa a Shanghai
2010-04-20 16:15:09 cri

Tsarin dakin Macao ya yi kama da wani kyakkyawan "Zomo", an yi amfani da wani gilashi na musamma a waje, saboda haka, launinsa yana iya canjawa.

Dakin Taiwan ya kunshi wani gini mai kama da dutse, da wata babbar fitila da aka rufa a sama wadda aka yi ta da gilashi, da wani na'ura mai kama da kwallo da take nuna fina-finai.. An bayyana cewa, an tsara dakin Taiwan ne bisa wata fitala ta gargajiya ta kasar Sin da wani mashahurin masanin ilmin soja na gargajiya mai suna Zhu Geliang ya kirkiro. A lokacin bikin baje koli, dakin Taiwan zai kunna wannan babbar fitila, tare da nuna fatan alheri da samun sa'a, kuma za a iya kallon fina-finai ta wannan na'ura mai kama da kwallo.

To, yanzu ga tambayoyi guda biyu game da gasarmu ta kacici-kacici. Tambaya ta farko, wace rana za a bude bikin baje koli na Shanghai? Tambaya ta farko, wace rana za a bude bikin EXPO na Shanghai? Tambaya ta biyu, mene ne launin dakin kasar Sin na bikin EXPO na Shanghai? Tambaya ta biyu, mene ne launin dakin kasar Sin na bikin EXPO na Shanghai?

Muna jiran amsoshinku ta wannan adirishi,

China Radio International

PMB 758

Garki, Abuja, Nigeria


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China