in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Hai Bao" za ta jagorance ku wajen yin ziyara a rumfar kasar Sin ta bikin baje koli na kasa da kasa a Shanghai
2010-04-20 16:15:09 cri

Dakin yankunan kasar Sin shi ne daki na larduna daban daban na kasar Sin, tsarinsa ya kunshi al'adun kasar Sin sannan yana kunshe da dukkan lardunan kasar Sin. Idan ka ziyarci dakin yankunan kasar Sin, za ka fahimci yadda al'adu da zaman rayuwar jama'a na wurare daban daban na kasar Sin suke.

Ban da haka kuma, "Hai Bao" za ta jagorance ku wajen yin ziyara a dakunan Hong Kong, da Macao, da Taiwan. Babban take na dakin Hong Kong shi ne "birni maras shinge", wannan ya kunshi salo na musamman guda shida na Hong Kong, an kebe shi a wurin na musamman da kyawawan manyan gine-gine, yana nuna huldar da ke tsakanin babban yankin kasar Sin da kasa da kasa, da kyawawan wuraren zirga-zirga, da fasahohin sadarwa na zammani, da musayar kudi da kayayyaki da bayanai ba rufa rufa, da musayar al'adun kasar Sin da kasashen Turai, da kyakkyawar zaman rayuwar birni.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China