in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Hai Bao" za ta jagorance ku wajen yin ziyara a rumfar kasar Sin ta bikin baje koli na kasa da kasa a Shanghai
2010-04-20 16:15:09 cri

Sannunku, sunana "Hai Bao", wato 'yar tsana da ke kawo alheri a yayin bikin baje koli na kasa da kasa wato EXPO a birnin Shanghai. Za a bude bikin EXPO a ran 1 ga watan Mayu, a cikin kwanaki fiye da 180, da za a shafe ana bikin, "Hai Bao" za ta yi wa mutane maraba da zuwa bikin EXPO daga wurare daban daban na duniya. Yanzu "Hai Bao" za ta jagorance ku domin yin ziyara a rumfar kasar Sin. Rumfar kasar Sin dai tana cibiyar farfajiyar bikin EXPO, ta kunshi dakin kasar Sin, da dakin yankunan kasar Sin, da dakunan Hong Kong, da Macao, da Taiwan. An lakabawa dakin kasar Sin sunan tambarin kasar Sin, wani wurin da ake iya ganin al'adun kasar Sin, da tunanin Sinawa, da salo na musamma na Sinawa na zamani.

Dakin kasar Sin shi ne daki mafi girma a farfajiyar bikin EXPO, muraba'in jinkar dakin ya kai filayen wasan kwallon kafa biyu da rabi. Dakin kasar Sin yana da salon kasar Sin a ciki da wajensa, kuma lauyin dakin kasar Sin ja ne, yana da tsarin ginin gargajiya na kasar Sin, tsarinsa ya yi kamar "Dou Guang", wato hular sarki na gargajiya.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China