Kullun yankunan Sahel-Sahara na Afirka suna fama da bala'in fari, wannan bala'i zai haddasa hasarar hatsi sosai, amma idan an yi amfani da maganin kashe fari za a gurbata muhalli. Saboda haka, kasar Senegal ta nazarin wani maganin kashe fari da aka kera da wasu halittu, wannan magani ba zai gurbata muhalli ba. Watakila nan gaba za a kara yin amfani da wannan magani a kasar Senegal da kasashen makwabcinta.
Yayin da shugaba Abdoulaye Wade na kasar Senegal ke halarci wannan taron nune-nune, ya ce, gwamnatin kasar Senegal tana mai da hankali sosai kan nazarin kimiyya da sababbin fasahohi, yawan kudin da ta samar kan wannan fanni ya karu daga dalar Amurka miliyan 8.5 na shekarar 2000 zuwa dalar Amurka miliyan 34. ya nuna cewa, gwamnati za ta ci gaba da nuna goyon baya ga ayyukan nazarin kimiyya da sababbin fasahohi, za ta ci gaba da neman raya kasa ta hanyar kimiyya da fasahohi. [Musa Guo]