Bisa bayanin da aka yi kan fannin fasahar makamashi, kasar Senegal wadda ke fama da karancin albarkatun kasa ta kan sayen man fetur da yawa daga ketare a ko wace shekara, amma kasar Senegal tana da yawan makamashin hasken rana, a kan kiranta "kasar rana". Saboda haka, gwamnatin kasar Senegal tana shirya bunkasa fasahohin yin amfani da makamashin hasken rana domin fama da karancin wutar lantarki, da kuma rage fitar da abubuwan da ke gurbata muhalli, haka kuma za a iya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Senegal.
Wanson Bado daga cibiyar nazarin shinkafa na Afirka wanda ya halarci wannan taro ya bayyana cewa, a cikin shekarun baya, saboda an fara shuka shinkafa mai samar da hatsi da yawa da fasahohin aikin gona masu ci gaba, kasar Senegal ta sami sabuwar hanya wajen fama da matsalar karancin hatsi. Ya ce, kasar Senegal tana bukatar shinkafa ton dubu 900, amma da ma ta kan fatar da shinkafa ton dubu 300 da kanta, ta kan sayen shinkafa da yawa daga ketare. Saboda haka, an fara shuka shinkafa mai samar da hatsi da yawa a arewacin kasar. A shekarar bara, yawan hatsin da aka samm ya kai ninka sau biyu bisa na da. Ban da haka kuma, kwararren masanin ilmin aikin gona na kasar Sin suna yin gwajin shinkafa mai kyau da kuma horar da manoma a arewacin kasar Senegal, wannan ya kara yawan hatsi da aka samu a wannan wuri sosai. Watakila kasar Senegal za ta cimma burinta na samar da isashen hatsi da kanta a shekarar 2012.