A kwanakin baya, an yi taron nune-nune na cigaban kimiyya da sababbin fasahohi a karo na farko na kasar Senegal a Dakar, babban birni na kasar, da ganin wannan taron nune-nune, ana iya ganin cewa, wannan kasar da ke yammacin Afirka na kokarin neman bunkasuwa ta hanyar kimiyya da fasaha.
Hukumar nazarin kimiyya da fasahohi na yau da kullum ta kasar Senegal ta shirya wannan taron nune-nune. A yayin wannan taro, an nuna hotuna, da fim, da kayayyaki da yawa domin yin bayani sosai kan nasarorin da kasar Senegal ta samu daga wajen nazarin kimiyya masu tushe da sababbin fasahohi cikin shekaru 50 tun bayan da kasar ta samu 'yancin kanta. A yayin wannan taro, kayayyakin sadarwa na zamani, kayayyaki masu yin tsimin makamashi da na kiyaye muhalli, da fasahohin ke yin amfani da makamashin hasken rana, da makamashi maras gurbata yanayi, da maganganun kashe fari da aka kera da wasu halittu da kasar Senegal ta nazari da kanta, da shinkafar da ke iya samar da hatsi da yawa sun jawo hankali na mahalartar taro sosai.