A cikin shekaru 20 tun da aka kafa dangantakar diplomasiya dake tsakanin kasashen biyu, huldar siyasa dake tsakanin su ta yi ta samun bunkasuwa. Hu Jintao, shugaban kasar Sin da sauran shugabannin jam'iyyar kwaminis ta Sin da na gwamnatin Sin sun kai ziyara a kasar Namibia, kuma Sam Nujoma, shugaban da ya kafa kasar Namibia da Pohamba, shugaba mai ci na Namibia sun kai ziyara a Sin sau da dama. Kuma an samu sakamakon wajen yin hadin gwiwa, yawan kudin da aka samu wajen yin cinikayya a tsakanin kasashen biyu ya kai kudin Amurka dala miliyan 577 a shekarar 2009, kuma ya karu da kashi 9.8 cikin dari yayin da ake fama da rikicin kudi da tabarbarewar tattalin arziki a duk duniya. Zumuncin dake tsakanin jama'ar kasashen biyu ya rika zurfafa, kuma Sin ta tura masu aikin jinya zuwa Namibia don ba da aikin jinya a cikin shekaru 14 a jere. A shekarar 2009, matasan Namibia 22 sun samun kudin bonas din karatu na kasar Sin da yin karatu a kasar.
Dangantaka ta sada zumunci a tsakanin kasashen biyu ta samun bunkasuwa a cikin shekaru 20 da suka gabata. Yayin da yake bayyana fatansa ga makomar dangantakar, mista Jia Qinglin ya ce, "Muna da imanin cewa, idan mun ci gaba da hadin gwiwa kamar yadda muka yi a da, to, za mu ci gaba da bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kyau a nan gaba."(Asabe)