in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jia Qinglin ya halarci liyafar da aka yi don tunawa da ranar cika shekaru 20 da kafuwar dangantakar diplomasiya dake tsakanin Sin da Namibia kuma ya yi jawabi
2010-03-30 22:00:11 cri

A gun liyafar, mista Jia Qinglin ya yi jawabi, inda ya waiwayi tarihin kafuwar dangantakar diplomasiya dake tsakanin kasashen biyu, kuma ya darajanta huldar gargajiya dake tsakaninsu ta zama wani zakaran gwajin dafi. Ga abin da ya ce, "Idan mun waiwaye tarihin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a cikin shekaru 20 da suka wuce, ana iya ganin cewa, huldar gargajiya dake tsakanin kasashen biyu ta yi fama da kalubale da yawa, wannan ya zama dukiyar dakiya ta jama'ar kasashen biyu, kuma ya zama wani zakaran gwajin dafi ga hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afrika har da dukkan kasashe masu tasowa na duniya."

Yayin da yake taba magana kan zumuncin gargajiya dake tsakanin kasashen biyu, Sam Nujoma, shugaban da ya kafa kasar Namibia ya ce, "Huldar dake tsakanin Sin da Namibia tana da zumunci da hadin gwiwa mai karfi, kuma an kafa irin wannan dangantaka a lokacin da jama'ar Namibia ke fama da wahalar neman 'yancin kai da mulkin kai. Tun daga shekarar 1990 zuwa yanzu, kasar Sin ta rika zama abokiyarmu yayin da muke neman bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China