Jia Qinglin ya halarci liyafar da aka yi don tunawa da ranar cika shekaru 20 da kafuwar dangantakar diplomasiya dake tsakanin Sin da Namibia kuma ya yi jawabi
A ran 26 ga wata, Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin ya halarci liyafar da aka yi don tunawa da ranar cika shekaru 20 da kafuwar dangantakar diplomasiya dake tsakanin Sin da Namibia kuma ya yi jawabi. Mista Jia Qinglin ya waiwaiye sakamakon da aka samu wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tun da suka kafa dangantakar diplomasiya, kuma ya bayyana fatansa ga makomar huldar dake tsakanin kasashen biyu.
An yi liyafar tunawa da ranar cika shekaru 20 da kafuwar dangantakar diplomasiya dake tsakanin kasashen Sin da Namibia a ran 26 ga wata a Windhoek, babban birnin kasar. Mista Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin dake yin ziyara ta sada zumunci a kasar Namibia, da Sam Nujoma, shugaban da ya kafa kasar Namibia, da kuma Asser Kapere, shugaban kwamitin kasar Namibia sun halarci taron.
1 2 3