in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin yaki da aikace-aikacen cin hanci da rashawa
2010-03-12 17:46:31 cri

 

A yayin da kasar Sin ke kokarin kyautata tsarin yaki da cin hanci da rashawa, tana kara hunkuta masu yin laifuffuka. Ran 11 ga wata, Mr. Cao Jianming shugaban hukumar koli mai kula da kararraki ta jama'ar kasar Sin ya bayar da rahoto cewa, a shekarar bara, yawan ma'aikatan gwamnati da hukumomin kula da kararraki suka hukunta ya kai fiye da 2600, a cikinsu akwai manyan jami'a 8.

A taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin, firaminista Wen Jiabao na kasar Sin ya bayar da rahoto cewa, kasar Sin za ta ci gaba da mai da hankali kan aikin "yaki da cin hanci da rashawa", ya ce, "Dole ne jami'ai da ma'aikatan gwamnatoci a matakai daban daban, musamman ma manyan jami'ai su gabatar da yawan kudin da suke da su, da halin da iyalansu ke ciki, tare da karbar binciken hukumomin shari'a. da kafa jerin tsarin hunkuta da yin rigakafi ga aikace-aikacen cin hanci da rashawa."


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China