in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin yaki da aikace-aikacen cin hanci da rashawa
2010-03-12 17:46:31 cri

A yayin tarurrukan majalisu biyu da kasar Sin ta shirya a shekarar da muke ciki. Ana ci gaba da zura ido kan batun yaki da aikace-aikacen cin hanci da rashawa. A cikin shekaru da dama da suka wuce, kasar Sin ta gabatar da jerin sabbin matakai domin hukunta wadanda suka aikata laifin cin hanci da rashawa tare da yin rigakafin wannan matsala, kuma sau da dama ne shugabannin kasar Sin sukan jaddada cewa, za su kara yin aikin yaki da cin hanci da rashawa, musannam ma aikin gina tsarin "yaki da cin hanci da rashawa". Wasu kwararre suna ganin cewa, sakamakon wadannan matakai, da gwamnatin kasar Sin za ta cimma buri ne na "gudanar da ikon gwamnati a gaban jama'a".

A cikin shekaru biyu da suka wuce, an zura ido kan "tsarin ma'aikatan gwamnati na gabatar da yawan kudin da suke da su". Tun daga shekarar bara, an fara gwada wannan tsari a wasu wurare na kasar Sin. Mr. Huang Shaoliang memban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa yana ganin cewa, wannan tsari yana da amfani wajen yin rigakafin cin hanci da rashawa. "Bisa gwajin da aka yi a wasu birane, wannan tsari yana da amfani sosai, jama'a suna gamsuwa da sakamakon da aka samu."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China