in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin yaki da aikace-aikacen cin hanci da rashawa
2010-03-12 17:46:31 cri

 

A yayin da aka gwada tsarin yin rigakafin cin hanci da rashawa, kasar Sin ta gabata da wasu matakai a shekarar bara, kamar kara saurara ra'ayoyin jama'a. Mr. Chen Yunlong shugaban hukumar kula da kararraki ta lardin Zhejiang ya nuna cewa, an hukunta wasu manyan jami'ai sakamakon saurara ra'ayoyin jama'a. ya ce, "Yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar yanar gizo wani gwaji ne mai kyau, wannan zai kara yawan shaidun cin hanci da rashawa da hukumomin shari'a su kan samu, tare da daidaita ayyukansu na hukumta laifuffuka."

Mr. Chen Yunlong yana ganin cewa, ya kamata a kara bayar da ayyukangwamnati da bayanan gwamnati a gaban jama'a, da jawo hankalin jama'a wajen kara sanin yunkurin aikin gwamnati, da sa kaimi ga ayyukan gudanar da ikon gwamnati, wannan zai ba da gudummowa sosai ga aikin yaki da cin hanci da rashawa, tare da kiyaye adalci da daidaituwa. Mr. Cao Yisun shehun malami na jami'ar siyasa da dokoki ta kasar Sin ya yarda da wannan ra'ayi. Ya ci gaba da cewa, dole ne kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan batutuwa biyu yayin da take yaki da cin hanci da rashawa, da farko shi ne bayar da bayani a gaban jama'a, na biyu shi ne kyautata tsari.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China