Bugu da kari kuma, aikin raya muhimman ayyukan yau da kullum da Sin ke yi don kasashen Afirka ya samu amincewa sosai daga wajensu ba tare da kasancewar sharudan siyasa. Furofesa Femi Olufunmilade na kasar Nijeriya ya bayyana cewa, "kasar Sin tana dukufa kan taimaka wa Afirka wajen raya muhimman ayyukan yau da kullum, kamar shimfida hanyar dogo da hanyar motoci ta zamani, da kafa masana'antun samar da wutar lantarki da dai sauransu, amma ba ta kara ko wane sharadin siyasa ba kamar Asusun ba da lamuni na duniya da kuma bankin duniya."(Kande Gao)