Zhou Tianxiang, mataimakin babban manaja na kamfanin CCECC shi ne wanda ya gana ma idonsa yadda ake aiwatar da wannan shiri. Ya bayyana cewa, "Ina tunani a zahiri, cewar tsohon shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo ya nuna kauna sosai ga hanyar dogo, har ma ya mayar da hanyar dogo a matsayin mafarkinsa. A farkon shekara ta 2006, kasar Nijeriya ta gayyace mu domin tsara fasali kan tsarin hanyar dogo. Yayin da shugaba Hu Jintao ya kai wa kasar Nijeriya ziyara a watan Afrilu na shekara ta 2006, shugabannin kasashen biyu sun yi shawarwari kan aikin, inda Mr. Obasanjo ya gabatar da wata bukata kan cewa, ko kasar Sin za ta iya samar da taimako a fannin ba da rancen kudi, haka kuma an daddale yarjejeniya kan rancen kudi a wancan lokaci. A ran 30 ga watan Oktoba na shekara ta 2006, an sa hannu a kan kwangila a hukunce."