in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana dukufa kan taimaka wa Afirka wajen raya muhimman ayyukan yau da kullum
2010-01-26 15:19:51 cri

Daga baya kuma, sakamakon sauyawar ikon mulkin kasar Nijeriya da kuma canzawar farashin man fetur, an dakatar da aikin kyautata hanyar dogo ta kasar Nijeriya sakamakon karancin kudi. A karshe dai, bisa kokarin da bangarorin biyu suka yi ba tare da kasala ba, a watan Nuwamba na shekara ta 2009, Sin da Nijeriya sun daddale yarjejeniyar gudanar da aikin kyautata hanyar dogo ta Nijeriya a kashi kashi. Game da babbar ma'anar aikin, Adeseyi Sijuade, babban manaja na kamfanin hanyar dogo ta kasar Nijeriya ya bayyana cewa, "aikin kyautata hanyar dogo ta kasar Nijeriya wani muhimmin abu ne na raya tattalin arzikin kasarmu, kuma hakan zai taimaka wajen kara yawan guraban aikin yi, kana da rage cunkuson motoci da hadarin motoci."

Ba kawai makasudin kamfanin CCECC shi ne kyautata hanyar dogo ta kasar Nijeriya ba, hatta ma yana son koyar da abokai 'yan Nijeriya fasahohi da ilmi a fannin hanyar dogo. Bola Akinterinwa, wani shahararren kwararre dan kasar Nijeriya kan al'amuran duniya ya bayyana cewa, ta aikin kyautata hanyar dogo, kasar Sin za ta koyar wa jama'ar kasar Nijeriya fasahohi kan hanyar dogo, lallai wannan abu ne da kasar Nijeriya ta fi bukata. Kuma ya kara da cewa, "a fannin hanyar dogo, gyara tsoffin hanyoyin reluwe da kera sabbin wagunoni na fasinja wata hanya ce wajen musanyar fasaha. 'Yan kasar Nijeriya za su samu horaswa a wannan fanni domin samun ilmin kiyaye hanyar dogo. Don haka yanzu ba kawai mun kashe kudi don Sinawa su gudanar da aiki ba, a'a abu mafi muhimmanci shi ne za mu fahimci yadda ya kamata mu yi haka."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China