in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya cimma nasara a wajen ziyarar da ya kai wa kasar Morocco
2010-01-14 14:55:31 cri

A shekaru 3 da suka gabata, a karkashin tsarin dandanlin tattaunawa na hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afrika, huldar dake tsakanin kasashen Sin da Morocco ta rika samun bunkasuwa, abin da ya sa cinikin dake tsakaninsu ya karu cikin sauri. A gun taron ministoci na 4 na dandalin tattaunawa na hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afrika da aka yi a watan Nuwamba na shekarar bara, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya gabatar da sabbin manufofi 8 wajen yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika wadanda za a aiwatar shekaru 3 masu zuwa. Yang Jiechi shi ma ya tattauna tare da Taib Fassi Fihri kan aikin tabbatar da wadannan manufofi 8. A game da haka, Xu Jinghu ta bayyana cewa, "Kasar Morocco muhimmiyar memba ce ta dandalin tattaunawa na hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afrika. Hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin Sin da Morocco ta samu bunkasuwa cikin sauri. A matsayin wata kawar kasar Morocco, kasar Sin ta ba da taimako wajen gina filin saukar jiragen sama na Rabat da kuma sauran wasu ayyuka. Wani burin da ake neman cimmawa a wajen ziyarar Yang Jiechi shi ne gudanar da ayyukan dake biyo bayan shirin Sharm El Sheikh. A yayin ziyararsa, bangarorin biyu sun tattauna kan yadda za a gudanar da wadannan ayyukan da kyau. Kasar Morocco tana son yin kokari tare da kasar Sin don tabbatar da sabbin manufofi 8 da matsaya daya da suka cimma."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China