in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mohammed Lamin Turay wanda ke kokarin sada zumunci tsakanin Sin da Saliyo
2010-01-11 14:42:31 cri

Bayan da Mohamed Lamin Turay ya gama karatu a nan kasar Sin, bai koma kasar Saliyo ba, sai dai ya bude wani dakin cin abincin Afirka a Beijing. Game da dalilin da ya sa ya bude wannan dakin cin abinci, Turay ya bayyana cewa, "Ina tsammani, kasar Sin ta san Afirka abin da ya wajaba ne sabo da huldar da ke kasancewa a tsakaninsu. Kamar aure, idan ba a san juna ba, shi ke nan, za a gamu da matsaloli iri iri."

A ganin Turay, yin mu'ammala a tsakanin gwamnatocin kasashen Sin da Afirka, ba zai isa bukatun fahimtar juna da ake da su ba. Dole ne jama'a farar hula su yi kokarin fahimtar juna.

Sabo da yana iya samar da abincin Afirka mai inganci a nan Beijing, dakin cin abincin Afirka, wato "Gidan Turay" ya shahara sosai a Beijing. Lokacin da aka yi gasar wasannin motsa jiki ta Olympic a Beijing a shekarar 2008, Mr. Turay ya taba karbar kungiyoyin 'yan wasannin motsa jiki na kasashen Afirka. Sannan a watan Mayu na shekarar 2009, lokacin da shugaban kasar Saliyo ya kawo wa kasar Sin ziyara, Gidan Turay ne ya samar wa shugaban abincin da yake bukata. Daga baya, shugaban kasar Saliyo ya nuna yabo ga Turay sabo da yana kokarin yada al'adun kasar Saliyo da na sauran kasashen Afirka a nan kasar Sin. (Sanusi Chen)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China