in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mohammed Lamin Turay wanda ke kokarin sada zumunci tsakanin Sin da Saliyo
2010-01-11 14:42:31 cri

Turay ya bayyana cewa, garinsa yana wani karamin birnin da ke bakin iyakar kasa tsakanin kasashen Saliyo da Guinea. A shekarar 1978, wato lokacin da yake da shekaru 12 da haihuwa, wasu Sinawa sun taba gina gadoji 2 da suke hade kasashen Saliyo da Guinea a garinsu. Sabo da haka, tun wancan lokaci, ya fara tuntubar Sinawa. Sakamakon haka, a lokacin da yake karami, Turay ya yi fatan zai iya kawo wa kasar Sin ziyara bayan ya girma. Sabo da haka, a shekarar 1989, a karo na farko Turay ya zo kasar Sin domin koyon Sinanci da kuma kara fahimtar kasar Sin. Ya ce, a lokacin da ake cikin shekaru 80 na karnin da ya gabata, lokacin farko ne da kasar Sin ta soma aiwatar da manufofin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. A cikin shekaru da yawa da yake karatu da yin zama a kasar Sin, ya san yadda kasar Sin take samun ci gaba da sauye-sauye. Turay ya kara da cewa, "Yanzu birnin Beijing yana kasancewa kamar wani sabon birni. Amma, lokacin isowata a nan, babu kome. Galibin motocin haya kananan motoci ne da surorinsu sun yi kama da burodi. Amma yanzu, lokacin da wasu mutane suke kawo wa Beijing ziyara, sun ga wani birnin Beijing da ke da kyan gani sosai. Ba su san yaya birnin Beijing ya samu ci gaba, amma na sani."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China