in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ba ta ci gaba da yin shiru kan sauyawar yanayi ba
2009-12-15 14:19:28 cri

Irin wannan matsayi ya sake samun ingantuwa a yayin taron ministocin kasashen Afirka kan batun yanayi da aka yi a watan jiya a Habasha, inda wadanda suka halarci taron suka samu ra'ayi daya kan kin yarda da zartas da sabuwar yarjejeniya domin maye gurbin "takardar shawara ta Kyoto", da kuma yin kira ga kasashen duniya da su bai wa Afirka karin goyon baya ta fuskar kudi da fasaha domin dacewa da sauyawar yanayi.

Ko da yake wasu kasashe masu sukuni sun dakatar da ba da kyautar kudi da musayar fasaha, wasu kuma sun yi bayani ne kawai, ba su dauki hakikanin matakai ba, amma hadin kai da nuna dagiya da kasashen Afirka suka nuna sun sanya ba a ci gaba da raina wannan nahiya ba. A farkon watan Nuwamba, a yayin shawarwarin Majalisar Dinkin Duniya kan sauyawar yanayi da aka yi a birnin Barcelona, dukkan wakilan kasashen Afirka sun janye jiki daga dakin taron domin nuna wa kasashe masu wadata kiyayya saboda ba su son yin alkawarin rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da yawa.

Ko da yake watakila za a zargi wadanda suka janye jiki daga dakin taro, amma shugabannin kasashen Afirka ba su nuna da-na-sani ko kadan ba. Wani mai ba da shawara ga shugaban kasar Cote d'ivoire dangane da batun muhalli ya yi bayani ba tare da boye boye ba da cewa, a hakika sun fuskanci barazana, wasu kasashe za su sami damar zarginsu da kawo cikas ga shawarwari, amma kasashen Afirka na bukatar kasashe masu sukuni da su yi alkawari na gaskiya, saboda jama'ar Afirka mutane ne da suka fi fama da illa a sakamakon bala'in sauyawar yanayi. (Tasallah)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China