in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ba ta ci gaba da yin shiru kan sauyawar yanayi ba
2009-12-15 14:19:28 cri

A watan Agusta na bana, shugabannin kasashe 10 na Afirka sun tattauna a babban zauren kungiyar Tarayyar Afirka wato AU a kasar Habasha domin cimma matsayi guda da kasashen Afirka za su dauka a yayin babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyawar yanayi da ake gudanarwa a birnin Copenhagen. Sun kuma bayyana wa kafofin yada labaru fatansu na neman samun diyya daga hannun kasashe masu wadata saboda hasarar da suke yi a sakamakon sauyawar yanayi.

Meles Zenawi, firayim ministan kasar Habasha da ke jagorantar wakilan kasashen Afirka domin halartar taron Copenhagen yana daya daga cikin shugabannin Afirka da suka fi nuna jaruntakar bayyana ra'ayi kan sauyawar yanayi. A watan Satumba na bana, ya taba cewa, idan kasashen Afirka ba su iya ganin kasashe masu wadata sun ba su kudi domin rage hasararsu bisa abubuwan da ke cikin yarjejeniyar da za a zartas ba, to, mai yiwuwa ne kasashen Afirka za su ki amincewa da yarjejeniyar, kuma za su yi amfani da fifikonsu a duniya, wato yana kasancewa da kasashen Afirka da yawa, za su yi kokarin sanya yarjejeniyar ta zama haramtacciya, har ma sun yi shirin janye jiki daga dakin taron domin nuna kiyayya.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China