in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ba ta ci gaba da yin shiru kan sauyawar yanayi ba
2009-12-15 14:19:28 cri

A kwanan baya, kamfanin Barclays Group, wani shahararren kamfanin ba da hidimar kudi da ya kafa babban zaurensa a London, ya gabatar da wani rahotonn bincike, inda ya ce, idan ba a hana ci gaban sauyawar yanayi ba, to, a cikin dogon lokaci a nan gaba, sauyawar yanayi za ta jawo wa kasashen Afirka hasarar yawan GDP da ya kai misalin kashi 15 cikin dari a ko wace shekara baki daya. Bankin Duniya da kuma hukumar kula da hatsi da aikin gona ta Majalisar Dinkin Duniya wato FAO su ma sun ba da sabbin rahotanni da cewa, Afirka da ke dogaro da yanayi matauka wajen raya aikin gona za ta fuskanci babbar hasara a sakamakon sauyawar yanayi, haka kuma, kasashen Afirka za su gamu da tsananin barazana wajen samun isasshen abinci.

A sakamakon fuskantar irin wannan hali mai ban tausayi, kasashen Afirka ba su so ci gaba da yin shiru ba, sun nuna hazaka sosai sun shiga shawarwari kan sauyawar yanayi da kuma ayyukan tsara ka'idojin kasa da kasa. Samun ra'ayi daya da neman samun diyya da kuma damar ci gaba da kasancewa a duniya sun kasance babbar murya da kasashen Afirka suka yi magana da ita kan batun sauyawar yanayi.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China